Amfanin Ganyen Magarya 5 A Jikin Dan Adam
Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi. Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfanin ta da irin cututtukan da take magani.
Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya.
Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikin su:
Ciwon Daji
A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature.
Miki Ko Kuraje
Sai a tafasa garin magarya da ruwan khal sai a wanke mikin ko kurjin da kyau da wadannan ruwan sai a marmasa garin magarya kadan a kan mikin bayan ya wuni a haka sai a saka ruwan dumi a wanke maganin sai a sake maimaitawa. In sha Allahu za a samu sauki.
Cutukan Ciki
Kama daga kumburin cikin da baya da alaka da cin wani abinci ko abin sha, zafin ciki da yawan tsuwar hanjin ciki akai akai sanadiyyar wasu kwayoyin cuta na bacteria sai a nemi ganyen magarya mai kyau a sabe sai a saka ruwan dumi a tace da kyau a sha kashi daya daga cikin kashi uku na karamin kofi. Haka za a maimaita da yamma.
Saurin Warke Ciwo
Anan, idan ana fama da jinya ko a lokacin da ake farfadowa daga wata rashin lafiya wacce ta kontar da kai a sanda kake jin jikinka ba karfi ko kaji baka son cin komai saboda baka jin dandanonsa. To sai ka nemi garin diyan magarya kamar cokali uku kanani sai ka sanya zuma ka kwaba ka sha.
Za ka rinka yin haka a kalla sau biyu ga wuni a cikin kankanin lokaci za ka ji karfi da kuma dadin jikinka. Ko kuma mafi sauki ka nemi diyan magarya ka dunga sha. A hakika suna kumshe da dimbin sinadirran bitamin C wanda yake hura garkuwar jiki fiye da wanda ke a cikin bitamin C din da muke siya a kemis din saida magani.
Yakar Cutukan Fata
Ganyen magarya na da karfin yakar cututtukan fata, kama daga da kazzuwa da kurajen fata na ba gaira ko ake kallon kamar na iska ne.