Amfanin Ganyen Gwaiba Ga Lafiyar Jiki

Yawancin mutane sun san amfanin ƴayan itacen gwaiba (Guava) zasu iya yi ga lafiyar mu. Amma ba dukan mutane ne suka san gaskiyar cewa ganyen gwaiba yana da sinadaran magani da yawa dake da fa’idodin kiwon lafiya ba.

Ganyen gwaiba yana da kyau domin kasancewar ku cikin koshin lafiya da kuma jin daɗin ku.

Ganyen gwaiba yana sinadarai masu yawa kamr bitamin da sauran wasu sanadarai masu masu yaƙi da wasu rashin lafiyoyi da dama. Waɗannan ganyen suna da ƙarfi na antioxidants.

Ganyen gwaiba yana cike da abubuwan hana kumburi da yaƙi da ƙwayoyin cuta kuma suna da manyan fa’idodi, wanda za’a iya amfani da su a matsayin magajin kashe zafin ciwo, kamar irin su ciwon gaɓoɓi.

Ganyen gwaiba na iya zama kamar mara amfani amma fa’idodin kiwon lafiyar shi suna da yawa, da suka ƙunshi babban adadin bitamin C, Vitamin A, fibers lafiya, potassium da lycopene.

Shan shayin ganyen gwaiba yana da amfani ga matsalolin rashin lafiyoyi da dama, wadanda suka haɗa da ciwon suga (Diabetes), gaɓoɓi, fata, ciwon ciki da sauran wasu cututtukan da ke damun al’umma na yau da kullum.

Yin shayi da ganyen gwaiba yana wasu fa’idodi wadanda ba mu ambata a wannan maƙalar ba, ciki har da kara kuzari ga ma’aurata a lokacin saduwar aure.