Amfanin Ƙwai Wajen Magance Ƙurajen Fuska
A yau zaku koyi yanda ake amfani da kwai wajen magance kurajen fuska wadanda aka fi sani da suna ‘Pimples’ a turance. A hakikanin gaskiya kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuskar mutane musamman a tsakanin mtasa mata da maza.
Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskar mu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.
Ababen da za a bukata:
• Kwanuka biyu.
• Kwai daya.
• Takardar ‘tissue’ daya.
Amfanin kwai ga fuska:
•Ruwan kwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma ‘minerals’.
• Yana kare fuska daga kuraje.
• Yana kuma rage tsufar fuska.
• Kara wa fuska haske.
• Rage kumburin ido.
A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.
Hadi: A fasa kwai sai a cire gwaiduwar. A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa. Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.
A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu. A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan? Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska.
Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar. Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.