Abu 3 Da Ya Kamata Ku Riƙa Sha Domin Tsaftace Ciki Da Cire Guba
Ciki wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin dan Adam. Yana karɓar abinci daga oesophagus. Lokacin da abinci ya isa gefen oesophagus, yakan isa ciki ta hanyar kwararo na tsoka da ake kira zurfin oesophagal sphincter.
Nazari ya nuna cewa ciki yana fitar da acid da enzymes masu narkar da abinci. Tunda gaɓar jiki ce mai laushi, ya kamata mu yi ƙoƙari mu kiyaye lafiyar ta.
Kayan sha daban-daban na iya taimakawa wajen tsaftace ciki da cire gubobi daga jiki. Wasu daga cikinsu sun hada da;
1. Shayin Farin Yaji (Ginger): Shayi farin yaki shine abin sha mai kyau ga ciki. Shayi shayin farin yaji shahara saboda yuwuwar sa don kwantar da al’amuran narkewar abinci musamman don taimakawa rage tashin zuciya.
Har ila yau shayin farin yaji yana taimakawa wajen cire guba daga cikin ciki idan an sha shi don haka a kai a kai.
2. Shayin Ganyen Zogale: Wannan abin sha yana taimakawa wajen wanke ciki. Shayi ko ruwan zogale na iya taimakawa wajen magance wasu cututtukan ciki kamar rikicewar ciki, gastritis, da ulcerative colitis.
Bincike ya nuna cewa maganin kashe kwayoyin cuta na zogale na iya taimakawa wajen hana samuwar cututtuka masu yawa, kuma yawan sinadarin bitamin B na taimakawa wajen narkewar abincj. Kowa yayi kokari ya saka wannan abin sha a cikin abincin sa.
3. Tafarnuwa: Wannan sinadari kuma yana taimakawa wajen wanke ciki.
Bincike ya nuna cewa sinadarin tafarnuwa na hana damuwa yana taimakawa wajen dakatar da karuwar yawan acid a cikin ciki da kuma tabbatar da tsafta da ingantaccen tsarin narkewar abinci.
Ya kamata kowa ya sanya tafarnuwa a cikin abincin sa.