Abinci Na Yau Da Kullum Wanda Ke Cutar Da Jikin Mu Idan Ba A Kula Ba
Kamar yanda muka sani ba zamu iya yin wasu muhimman ayyuka ba tare da mun ci abinci ba, abinci shine matsayin mai wanda yake tafiyar da mu a yau da gobe.
Abinci da yawa kan iya janyo rashin lafiya a jiki idan har ba’a kula da kyau ba.
Ga jerin abinci da ka iya haddasa rashin lafiya ga jikin mu nan kasa;
1. Abinci Masu Saukin Dafawa;
Ko kun san cewa ire-iren wadannan abincin masu saurin girkuwa kan iya hana nau’in abinci mai kyau yin amfani a jikin ku?
Ire-iren wadannan abincin, baya ga yawan suga da suke kunshe da shi, sukan iya kawo ciyon hawan jini (Diabetes), kana kuma su kawo canje-canje a kwakwalwar ku.
2. Kayan Shaye-Shaye Na Ruwa (Lemuka);
Shan irin wadannan lemukan masu dauke da sanadarin (Soda) kan haddasa wani rashin lafiya nauyin ciyon suga na biyu (Diabetes 2).
Kuma sukan iya haddasa kiba mara kima, dalilin suga mai yawan da suke dauke da shi.
3. Abincin Da Aka Sarrafa;
Saboda son yin sauri domin kawar da yunwa, abu ne mai sauki mutum ya samu abinda zai shirya a nan take, ko cikin mintuna goma a wannan zamani.
Mafi yawancin irin wadannan abincin da aka riga aka sarrafa sun kunshi wadansu sinadarai masu hatsari a cikin su, kamar (Soda), (Fat) da ma sauran sinadarai masu sanya abincin ya dade a ajiye bai lalace ba, kamar kifin gwangwani da makamantan shi.
4. Jan Mana;
Cikin jan nama ko kasuwancin sa abune wanda aka dauki shekaru aru-aru ana yin sa, kuma kullum sai karuwa yake.
Ga wadansu daga cikin mu dake son cin nama a koda yaushe, su sani cewa bincikr ya nuna akwai nau’in cutar daji (Cancer) ya iya haddasawa.
Mussamman ma nama shanu.