Bayanin Sabuwar Wayar ‘Infinix Hot 12’

Lokaci da daɗewa, kamfanin Infinix ya kasance yana haɓaka matakai daban daban don abin da ake nufi na samun karɓuwa da salon rayuwa mai daɗi ta fannin kimiyya ‘Technology’.

Sabuwar waya a cikin jeri na na’urori ita ce Infinix Hot 12, kuma kamfanin bai gaza a nan ba.

Wayoyin Hot Series sun zo dauke da Helio G85 processorand, 5000 mAh wanda ke ba da nishaɗi mara tsayawa da ƙwarewa mara iyaka a wasanni ‘Games.

Infinix Hot 12 kuma ta fito da ƙira mai ɗorewa tare da 90 Hz nunin saurin aiki. Wannan yasa wasan Games ya zama mai daɗi.

Masu amfani da wayar kuma suna jin daɗin yin caji mai sauri tare da cajin Infinix Hot 12 mai sauri na 18w don cigaba da jin daɗin amfani na tsawon rana.

Infinix Hot 12 ta fito tare da 6GB RAM da 128GB memorin ajiya wanda ake iya faɗaɗawa ta hanyar microSD ko Memory Card.

Wayar kuma tana aiki ne akan version na Android 12 tare da XOS 10.6.