Tarihi

1983: Yadda Aka Kashe Mutumin Da Yayi Kokarin Kama Tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari

Yana da kyau a dawo da tarihi don manufar samari, don ba su damar yin koyi da kurakuran da wasu suka yi a baya, ta yadda za su gujewa yin haka idan suka sami kansu a kan madafun iko.

Kwarewa ita ce mafi kyawun darasi ga rayuwa.

Birgediya Ibrahim Bako wanda ya rayu tsakanin 1941 zuwa 1983, an zabe shine ya kamo shugaba Shehu Shagari saboda mahaifinsa abokin shugaban kasa ne.

Bako dai bai sani ba, an fallasa juyin mulkin ga Shagari kuma masu gadinsa suna cikin shiri.

An kashe shine a lokacin da yake yunkurin kama shugaban kasar a juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga watan Disamba, 1983 wanda ya kawo Manjo-Janar Muhammadu Buhari kan karagar mulki.