Ɗan Tawayen Farko A Najeriya Kafin Ojukwu Yayi Yunkurin Kafa Kasar Biyafara

Da dama daga cikin yan Najeriya na ganin cewa ɗan Najeriya na farko da yaso ballewa, shi ne Odumegwu Ojukwu lokacin da ya ayyana kafa kasar Biyafara a shekarar 1967.

Sai dai kuma kafin Ojukwu ya kasance an yi ɗan gwagwarmaya mai suna Adaka Isaac Boro (1938_1968), wanda ya ayyana jamhuriyar Neja Delta a shekarar 1966.

Da farko Adaka Boro dalibi ne na farko a fannin ilmin sinadarai kuma shugaban kungiyar dalibai na jami’ar Najeriya Nsukka. Sai dai ya bar makaranta ne domin ya jagoranci zanga-zangar nuna adawa da yadda ake hakar mai daga yankin Neja Delta a Najeriya.

A cewar shi, hakar man fetur din ya amfanar da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin yankin gabas wanda babban birnin ta ke Enugu. A ra’ayin shi, ya kamata a baiwa al’ummar Neja Delta kaso mafi yawa na kudaden da ake samu daga man fetur din saboda an hako mai daga yankin su.

Daga nan sai Adaka Boro ya kafa rundunar sa kai ta Neja Delta, wadda ta kunshi yan kabilar Ijaw, suka kuma shelanta jamhuriyar Neja Delta a watan Fabrairun 1966.

Boro da mutanen shi sun yi yaki da sojojin gwamnatin Tarayyar Najeriya na tsawon kwanaki 12, amma daga baya aka ci su da yaƙi, aka kama su.

Wadanda suka cafke su dune sojoji karkashin gwamnan mulkin soja Aguiyi Ironsi, wanda ya yanke musu hukuncin kisa bisa samun su da laifin cin amanar kasa.

Kafin Adaka Boro ya dauki makami da gwamnatin mulkin soja ta tarayya, mahaifin shi wanda ya kasance mai ilimi tun da farko ya yi masa alkawarin karbar tallafin da yayi masa na daukar nauyin karatu a wata jami’ar kasar waje. Sai dai matashin Boro ya ki amincewa da wannan tayin da mahaifin shi yayi masa, ya cigaba da yakar gwamnatin tarayya.

Daga baya mahaifin shi ya cigaba da yaki a bangaren Najeriya a lokacin yakin basasar Najeriya, amma daga baya ya rasu a watan Mayun 1968 ba tare da sanin komi ba a garin Ogu na jihar Ribas.

A karshe, makasudin wannan labarin shi ne don ilimantar da jama’a da kuma tunani, ba don haifar da rashin hadin kai ko raba kan yan Nijeriya ba. Don haka ina kira ga masu karatu su karanta don ilimi da tunani.