Ɓawon Abarba: Babban Maganin Gargajiya Domin Ciwon Gaɓoɓi
Ruwan tafasasshen ɓawon abarba magani ne mai ban sha’awa na yanayin domin kula da cututtukan ciwon gaɓoɓi.
Bawon abarba ya ƙunshi sinadarin bromelain, wani kemikal mai dauke da sinadarai masu hana zafi da kumburi wanda zai iya taimakawa wajen rage raɗaɗi da zafi da kumburin da ke da alaƙa da amosani, ko ciwon gabbai.
Ta hanyar tafasa bawon abarba, domin fitar da ruwan masu amfani, yana haifar da abin sha mai gina jiki da warkar da ciwon gaɓoɓi da sauran cututtuka.
Yin amfani da ruwan dafaffen ɓawon abarba akai-akai na iya ba da taimako ga mutanen da ke fama da ciwon amosanin gabbai, tare da samar musu da hanyoyin da za su iya kula da yanayin rashin lafiyar su.
Kawai a tafasa ɓawon abarba a tukunya na tsawon mintuna 15, sannan a bar ruwan ya huce, za’a rika shan karamin kofi biyu kowace rana.