Tarihi

Ƙasar Da Ba A Taɓa Yin Zaɓe Ba A Afrika Tun Bayan Samun Ƴancin Kan Ta

Mutane da yawa sun yi tunanin cewa al’amura zasu yi zafi ga wata ƙasa domin sun yi yaƙi kuma sun sami yancin kai. Amma zai zama abin mamaki idan aka fahimci cewa mutanen da suka yi gwagwarmayar neman yancin kai sune suke zaluntar su.

Akwai ƙasashe da yawa a Afirka waɗanda ke aiwatar da mulkin demokraɗiyya, Eritrea ba ta cikin su. Duk da cewa suna da jam’iyyar siyasa, amma su kadai ne ke kan mulki tun daga shekarar 1991.

Ga wanda bai san ko wane ne shugaban kasar Eritiriya ba, sunan shi Isaias Afwerki, ya jagoranci mayakan yantar da al’ummar Eritiriya zuwa nasara a kan kasar Habasha a shekarar 1991.

Tun bayan zaben shi da yan majalisar dokokin kasar suka yi a shekarar 1993, ba’a taba yin zabukan gama gari da aka gudanar tun wancan lokacin.

Shugaban kasa yana da ikon majalisa da na zartaswa a hannun shi, wanda hakan yasa ba za’a iya tsige shi ko kiran zabe ba.

Ba zai zo da mamaki ba idan aka fahimci cewa kasar ba ta da tsarin shari’a mai zaman kan shi, duk ya rataya ne a kan yatsan shugaban kasa.

Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe sun yi Allah wadai da matakin, inda suka bayyana kasar a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi danniya a duniya.

Rahoton ya bayyana cewa kasar ta rufe dukkanin kafafen yada labarai masu zaman kan su da za su iya kalubalantar ikon shugaban kasar, tare da kulle duk wani nau’i na adawa da zai iya adawa da mulkin shi. Shugaban ya kewaye kan shi da wasu ƴan ƴan sa-kai da wasu ƴan mutane da aka sani masu biyayya, suna aiki da umarnin dhi ba tare da tambaya ba.

Shugaban Eritrea mutum ne mara tausayi, yana murkushe yan adawar sa ba tare da nadama ba. Mutane da yawa sun zarge shi da mulkin kama-karya, inda suka yi tir da shi bisa laifuka da dama na cin zarafin dan Adam. Don haka da yawa daga cikin yan kasar na yin kasada da rayukan su don gudun hijira daga wannan kasa zuwa Gabas ta Tsakiya ko kuma Turai.