Tarihi

Ƙabarin Sayyidina Hamza R.A

Misalin shekaru 70 da suka gabata, ruwayoyi da dama sun nuna an yi wata ambaliyar ruwa a filin Uhud wanda yayi sanadiyar cikan kaburburan Sahabbai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ruwa.

An habarto cewa Sheikh Mahmud Sawaf na daga cikin wadanda suka hako kaburburan Sahabbai domin canza musu wuri, yace yaga jikin Sayyiduna Hamza (R.A) ya ce:

Allah ya kare jikin shi har da likafanin da aka rufe shi da ita ba tayi komai ba, yace Hannun shi yana rike da cikin shi daidai wajen da aka ji masa rauni, ya ce, da suka daga hannun shi, nan take jini ya kama zuba kamar lokacin aka ji masa rauni.
Wannan shine Kabarin Zakin Allah Sayyiduna Hamza (R.A).

Allah ya kara musu kuma kasa mu yi kyakyawan karshe kasa mu cika da kalmar shahada.

Allah shi ne mafi sani!