Addini

Yadda Ake Yin Muraji’ar Alkur’ani Mai Girma

Alqur’ani yana bukatar muraja’a kuma idan mutum ba ya yin muraja’a zai iya manta duk abin da ya haddace, saboda shi al-qur’ani kamar rakumi ne idan ka rike akalarsa sai ya bi ka, idan kuma ka sake shi sai ya gudu, don haka idan mutum ya haddace alqur’ani yana da babban aiki akansa na yawan maimaita abin da ya haddace, kamata ya yi ka dinga hada hadda da muraja’a a lokaci daya don kar kana haddace wani wuri na baya yana rushewa, daga cikin hanyoyin muraja’a akwai:

  • Idan zai yiwu ka kasa al-qur-ani gida uku, kashin farko daga suratu Annas zuwa Ankabut, kashi na biyu daga suratul Kasas zuwa Yunus, kashi na uku daga suratu Attaubah zuwa Bakara.
  • Idan ka haddace izu ashirin, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata kana maimaita shi, wannan zai taimaka wajan karfafa haddarka.
  • Idan ka haddace izu arba’in, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata biyu kana maimaita shi, wannan zai sa haddarka, ta yi kwari.
  • Idan ka haddace al-qur’ani gaba daya ka yi kokari ka matsawa kanka, wajan yin bitar wani bangare na al-qur’ani kullum, kamar izu biyu kulum ko makamancin haka, duk kuma ranar da ba ka yi ba, ka yi kokari ka rama. Duba khuduwatun ilassa’adah 195-196.

Dr Jamilu Zarewa
20/9/2012