Wani Ɗan Arewa Ya Ƙirƙiri Sabon Bankin Intanet, ‘Kayi Bank’

Wani daga Arewacin Najeriya ya kirkiri sabon bankin intanet mai suna Kayi Bank.

Bunkunan intanet kamar Opay, Kuda da kuma Moniepoint sun samu wani abokin gogayya a wannan fagen da zai fafata da su.

Shahararren dan kasuwa a Kano, Alhaji Sa’adina Dantata ya kirkiri sabon bankin zamani na intanet, ‘Kayi Bank’.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Bosun Tijjani ya kaddamar da bankin zamani na intanet mai suna ‘Kayi Bank’. Bankin wanda attajirin dan kasuwa, Alhaji Saadina Dantata ya dauki nauyi an kaddamar da shi a Abuja a makon da ya gabata.

Arewa Times ta tattaro cewa bankin Kayi kasashe da dama kamar su Daular Larabawa da Turkiyya da Saudiyya sun zuba hannun jarin su a cikin shi.

Da yake magana a wurin kaddamar bankin, Sa’adina Dantata, ya ce an samar da kamfanin ne don shawo kan matsalar fasaha da tsaro da kuma inganta jin abokanan hulda.

Daga: Abdulrashid Abdullahi Kano