Kasuwanci

Kasashen Afrika 10 Masu Noman Shinkafa Sosai A Shekara

A ƙasa akwai jerin sunayen ƙasashe masu samar da shinkafa dake a nahiyar Afirka a duk kowace shekara.

Wadannan kasashen dake noma wannan shinkafa ba wai kawai domin amfanin cikin gida ba suke noma shinkafar ba, har ma suna fitar da ita zuwa wasu ƙasashen nahiyar kamar Jamhuriyyar Nijar da sauran su.

1. Najeriya 🇳🇬 – kimanin ton miliyan 8.3

2. Masar 🇪🇬 – ton miliyan 4.9

3. Madagascar 🇲🇬 – aƙalla ton miliyan 4.4

4. Tanzaniya 🇹🇿 – adadin ton miliyan 2.7

5. Guinea 🇬🇳 – kimanin ton miliyan 2.5

6. Mali 🇲🇱 –  ton miliyan 2.4

7. Saliyo 🇸🇱 – adadin ton miliyan 2

8. Cote d’Ivoire 🇨🇮 – ton miliyan 1.7

9. DR Congo 🇨🇩 – ton miliyan 1.6

10. Senegal 🇸🇳 – tana da ton miliyan 1.4

Bugu da kari, wannan adadin na iya canjawa a kowane lokaci, musamman ganin yadda karin al’umma ke rungumar harkokin noma iri-iri, kama daga noman rani zuwa na damina saboda yadda kayan abinci ke tashin gwauron zabi.

Advertisement