Kasuwanci

Sabon Farashin Buhun Siminti (50g) A Najeriya

Yawan canjin farashin siminti a Najeriya a yan kwanakin nan ba tare da an sanar da mutane da injiniyoyin da abin ya shafa ba abin damuwa ne matuka.

Injiniyoyin masu gine-gine da sauransu basu da wani zaɓi da ya wuce bin yanayin sauyin farashi ta yadda za a cigaba a yadda abubuwa suka zo.

Wannan saboda, galibin gidajen da aka gina a Najeriya suna amfani da buhunan siminti masu yawa tun daga kwandishin har zuwa gina.

Kudin buhun siminti mai nauyin kilogiram 50 a Legas ko Fatakwal ba irin farashin da dillalai ke sayar da shi a Abuja, Kano, Sokoto ko wasu Jihohin Najeriya ne ba.

A halin da muke na shekarar 2024, farashin buhun siminti kamar Ɗangote da sauran sannannun kamfanonin ya tashi daga ₦7,800 zuwa ₦8,500 amma kuma ya danganta daga jaha ko yanki zuwa yanki.

Tunatarwa: Kuɗin buhun siminti kafin haɗa wannan rahoton a duk faɗin Najeriya sun tashi daga ₦7,800 – ₦8,500

Ku cigaba da kasancewa damu domin samun ƙarin bayani game da farashin siminti a kowane lokaci idan ya camja.