Jihohi 3 Da Suka Fi Kowace Jiha Noman Doya A Najeriya

A cikin wannan makala za mu duba Jihohi 3 da ke samar da doya mai yawa a Najeriya, a cewar Knoema.

1. Jihar Benue: Jihar Benue na daya daga cikin jihohin Arewa ta tsakiya a Najeriya.

Wannan jiha tana daya daga cikin manyan jahohin da suke noman doya a Najeriya.

Sauran amfanin gonakin kuɗi sun haɗa da wake, shinkafa, gyada, Rogo, da dai sauransu.

A cewar Knoema, noman doya a Benue ya kai metric ton 2,866 1000 a shekarar 2006.

2. Jihar Taraba: Taraba jiha ce da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya, mai suna da sunan kogin Taraba da ya ratsa kudancin jihar.

Wannan jiha kuma tana daya daga cikin manyan jahohin da suke noman doya a Najeriya.

Ya zuwa 2006, noman doya a Taraba ya kai metric ton 2,694 1000, a cewar Knoema.

3. Jihar Niger: Niger jiha ce da ke a yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya.

Wannan jiha kuma tana daya daga cikin manyan jahohin da suke noman doya a Najeriya.

A shekarar 2006, noman doya ga Nijar ya kai metric ton 2,213 1000, a cewar Knoema.