Tarihin Mai Kuɗin Afrika Na Farko, Alhassan Dantata

A cikin shekarar 1940, Alhassan Dantata ya kasance mafi arziki a yammacin Afirka.

Ya yi aiki da goro, sannan ya gina dalar gyada a Kano. Kowane dala yana da jakunkuna 15,000 da aka cika.

Ya kasance mai ba da kayayyaki ga kamfanonin kasuwanci na Burtaniya.

Alhassan Dantata ya bude wani asusu a bankin British Bank of West Africa (yanzu First Bank) da tsabar azurfa 20 na rakumi a Kano, Nigeria a shekarar 1929.

Babban jikansa, Aliko Dangote shine Bakar fata mafi arziki a Afrika ta yamma.