Sunayen Allah 20 [1-20] Daga Cikin Sunayen Shi 99 Da Ma’anonin Su

Rukunin Imani (Imani) na farko a Musulunci shine Imani da Allah. A matsayin mu na musulmi, mun yi imani da Allah bisa kyawawan sunayen shi da siffofin shi. Allah ya saukar da sunayen shi akai-akai a cikin Alkur’ani mai girma da farko domin mu fahimci ko wane ne shi (Allah).

 • AR-RAHMAN – Mai Rahama
 • AR-RAHEEM – Mai jinkai
 • AL-MALIK – Mai mulki
 • AL-QUDDUS – Tsarkakke
 • AS-SALAM – Mai aminci
 • AL-MU’MIN – Mai bayar imani da aminci
 • AL-MUHAYMIN – Masani da kiyayewa akan komai
 • AL-AZEEZ – Mai karfi
 • AL-JABBAR – Mai tilastawa
 • AL-MUTAKABBIR – Mai buwayayyen karfi da girma
 • AL-KHAALIQ – Mai halitta
 • AL-BAARI’ – Ainahin mai kirkira
 • AL-MUSAWWIR – Mai fasaltawa
 • AL-GHAFFAR – Mai gafartawa
 • AL-QAHHAR – Mai mulki da mallaka
 • AL-WAHHAAB – Mai kyauta
 • AR-RAZZAAQ – Mai azurtawa
 • AL-FATTAAH – Mai budawa
 • AL-‘ALEEM – Masani komai
 • AL-QAABID – Mai rikewa