NLC Ta Dakatar Da Yajin Aikin Tallafin Man Fetur

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar a ranar Laraba.

Kungiyar ta dauki matakin ne a wani taro da wakilan gwamnatin tarayya a daren ranar Litinin a Abuja.

A ranar 2 ga watan Yuni ne kungiyar NLC ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki biyar kan ta koma kan tsohon farashin man fetur ko kuma ta fuskanci yajin aiki a fadin kasar biyo bayan karin farashin man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) yayi.

Sanarwar da Shugaba Bola Tinubu yayi na kawo karshen tsarin tallafin a yayin jawabinsa na kaddamar da shi a ranar Litinin da ta gabata ya biyo bayan dawowar dogayen layukan da aka yi a gidajen mai da kuma karin farashin man fetur da ‘yan kasuwa suka yi.

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan kan dakatar da yajin aikin ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce kungiyoyin sun amince da cewa dole ne NLC ta dakatar da sanarwar yajin aikin nan take domin a ci gaba da tuntubar juna kan lamarin.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata zantawa da yayi da manema labarai.

A ranar Litinin din da ta gabata ne kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja ta hana kungiyoyin kwadagon shiga yajin aikin.