Addini

Muji Tsoron Wutar Jahannama Domin Gujewa Azabar Ubangiji

Daga: Ali Abubakar Sadiq

Wannan hoton dake a sama, tumbin duniya ne da irin narkakkiyar wutar da ke ci a karkashin kasa, wanda zafin wannan wutar ya zarta zafin da rana ke da shi sosai. Zafin wutar da ke tumbin duniyan nan da muke ciki kuma muke taka doron kasa akanta, ya kai kimanin degree 6,000 na Celsius, yayin da zafin rana wacce muke gani a kullum degree 5,500 ne.

Idan za ka iya kwatanta wannan zafi da abinda ka sani, sai ka ce ya kai zafin ninkin tafasashshen ruwan-zafi (wanda 100° Celsius ne) sau 60 a takaice. Ka duba yadda tafasashshen ruwan zafi ke kwashe fatar dan adam kai tsaye. To Ina ga idan an ninka wannan zafin har zuwa sau 60 ya kai dan uwa?

Allah na fito mana da wannan narkakkiyar wuta da ke tumbin duniya lokaci zuwa lokaci, yayin girgizar kasa ko aman wutar dutsuwa a wasu yankuna na duniya (Volcanic eruption), ko kuma duk inda kogin wannan narkakkiyar wuta ya bi, sai ya narke komai a kan hanyarsa, walau dutse ko karafan dake ƙarƙashin kasa.

Wannan fa zafi ne na wannan duniya, ba irin na wutar Jahannama ne ba. Idan baka tsoron Ubangiji, to ka ji tsoron Jahannama, kuma kwana nawa ya rage mana a duniya zuwa lahira? Duk tereren ka, nan da shekaru, matuka shekara 100 ka san makomar ka, kowane ne kai.

Haka zalika, idan ka ga dama, ka yi alheri, in ka ga dama yi ta aikata teranci. Kai kadai aka haifa, kake rayuwa, kuma za ka mutu a saka ka kabari kai kadai, kuma kai kadai Allah zai yiwa hisabi ranar al-kiyama.

Sannan kuma daga karshe, a kiyamar zabi biyu ne kawai, aljanna ko wuta. Don haka zabi ya rage namu a nan duniya. A yi gaskiya, a kare gaskiya sannan a aikata ta. Ko kuma a bi karya, a kare ta tare da aikata ta. Akwai ranar murna ko ranar nadama.

Imma shakiran, wa imma kafura – Al Qur’an