Mene Ne “Savings Account” Da Aikin Shi?

Nasan wannan tambayar zata iya saka ku dariya, amma kuma waɗanda zata zama haske a gare wajen yanke shawara a wajen buda asusun ajiya na Banki.

Savings Account, ko kuma Asusun ajiyar kuɗi a turance shine asusun ajiya wanda aka buɗa don ajiye wasu da ba ku buƙatar ko shirin kashewa nan take. Wannan ya bambanta da asusun kai tsaye, wato “Current Account” a turance, wanda zai iya ba ka damar saka kudi cire su a nan take don yin sayayya ta amfani da katin zare kudi ATM.

Lokacin da kake son ware kuɗi don buƙatu da burin gaba, asusun ajiyar kuɗi zai iya zama mafi kyawun zaɓi gare ka.

Sannan kuma asusun ajiyar kuɗi yana ba ku damar saka kuɗi don adanawa yayin da kuke samun riba “Interest” akan balance din ku.