Mene Ne Inshora, Ya Take Aiki?

Insurance, a turance, ko kuma ‘Inshora’ a yaren Hausa, hanya ce ta sarrafa lasada ko hadari akan kadarorin ku.

Insurance yarjejeniya ce ta doka tsakanin ɓangarori biyu watau kamfanin Insurance (mai kamfanin) da mutum (mai inshora).

Lokacin da kuka sayi Insurance, kuna siyan kariya daga asarar kuɗi da ba zato ba tsammani.

Kamfanin Insurance yana biyan ku ko wanda kuka zaɓa idan wani mummunan abu ya sami kadarori da duniyoyin ku.

Idan ba ku da Insurance kuma wani haɗari ya faru kadarorin ku, misali Mota ko wani makamancin haka, za ku ɗauki alhakin duk abin ya sami duniyoy ko kadarorin ku wato (Assets) a turance.