Mene Ne “Current Account” Asusun Kudi Na Kai Tsaye?

Asusun ajiyar kuɗi na banki wato “Current Account” yan kasuwa ne masu yawan hada-hadar kudi ke buda shi. Sannan kuma yana bada damar tura kudade masu yawa a lokata maras adadi.

A cikin asusun “Current“, ana iya saka adadin kuma a cire shi a kowane lokaci ba tare da bayar da sanarwa ba.

Yayin da Asusu na ajiye “Saving” shine wanda a cikinsa kuke saka ajiyar ku a banki kuma ku sami riba akan kudin dake ajiye a ciki, shi kuma asusun na yanzu “Current” shine inda kuke saka kuɗi don gudanar da kasuwanci kuma ba’a samun a kudin koda an bar a cikin asusun.