Matsayar Magabata Akan Sha’anin Yazidu Dan Mu’awiyya
Tambaya: Assalamu Alaikum,
Dan Allah abani Amsar wannan tambayar:
Yazeedu d’an Mu’awiya ya matsayinsa yake a Musulunci? Daga mai bibiyar ku Masoyin ku daga Nijar. Bis’salam sai na ji ku.
Amsa: Wa’alaikum assalam wa rahmatullhi, Yazidu D’an Mu’awiya an haife shi ne a zamanin sayyadina Usman, don haka baya cikin sahabbai wadanda Allah ya tabbatar da adalcinsu.
Magabata nagari basa yabon Yazidu ba, kuma basu zaginsa.
Abin da yasa basa yabonsa shine; saboda shekaru uku da watanni kawai yayi yana mulki, a shekarar farko ta mulkin shi aka kashe Hussain jikan Manzon Allah s.a.w, duk da cewa ba shi yayi umarni da kashe shi ba.
Na biyu kuma aka jefi Ka’aba har sai da wani bangare ya kone, sannan ya karkare mulkinsa da yakar mutanen Madina, an kashe sahabbai da yawa a cikin yakin.
Abin da yasa basa zaginsa shine; saboda fadin Annabi S.A.W: “Farkon rundunar da za ta yaki Kusd’and’aniyya an gafarta mata”, Bukhari ya rawaito wannan hadisin a sahihinsa, kuma shi Yazidu Yana cikin wannan runduna, wannan yasa malaman suka tsaya cak akan lamuransa, suka fawwala su zuwa ga Allah, shi zai yi hukuncin da yaga dama da shi .
A takaice dai Yazidu yana da kurakurai wadanda suka hada da kashe mutanen Madina da kuma shan giya a wajan wasu maruwaitan, sannan Yana da kyawawan ayyuka Kamar yakar Birnin Sarki Kaisar, wanda hadisi ya tabbatar da gafara ga rudunar da yake ciki, wannan yasa tsunduma shi a wuta kacokan yake da wahala.
Don neman karin bayani duba Majmu’ul fatawa 4/481 da kuma Siyaru a’alamin nubala’i 4/38.
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
27/12/2021