Shekara 11 A Jere, Dangote Shi Ne Wanda Yafi Kowa Kudi A Afirka

Dan kasuwa Aliko Dangote ya cigaba da rike mukaminsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

Forbes, wata mujallar kasuwanci ce ta Amurka, da ta shahara wajen bin diddigin dukiyar attajirai a duniya.

“Shekara 11 a jere, Aliko Dangote na Najeriya shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar, wanda ya kai kimanin dala biliyan $13.9, sama da dala biliyan 12.1 a bara, biyo bayan karin kashi 30% na farashin hannayen jari na Simintin Dangote, kadarorinsa mafi daraja.”

Mujallar ta bayyana hakan ne a wani sakon da ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar litinin inda ta bayyana jerin sunayen attajiran Afrika na shekarar 2022.

Na biyu ga Dangote shi ne hamshakin attajirin nan na Afirka ta Kudu, Johann Rupert.

Wasu ‘yan Najeriya biyu da ke cikin jerin sun hada da Abdulsamad Rabiu (na biyar) da Mike Adenuga (na shida).

Forbes ta ce Mista Rabiu ya sami mafi girman karuwar arziki daga jerin shekarar da ta gabata.

hamshakin attajirin nan na Najeriya, Abdulsamad Rabiu, wanda ya fi dala biliyan 1.5 bayan ya dauki wani kamfani a bainar jama’a.