Addini

Makarantan Alkur’ani Mafi Kwarewa A Duniya

Al qāriʾ (Larabci: قَارِئ, ’mai karatu’, jam’i (قُرَّاء “qurrā” ko قَرَأَة “qaraʾa”), (makaranta Alkur’ani a harshen Hausa), mutum ne mai karatun al-qur’ani da sharuddan karatun na Tajwidi.

Ko da yake ana kwadaitar da shi, amma ba lallai ba ne makaranci ya haddace Alqur’ani baki daya ba, kwarewar shi ne karanta littafin Allah bisa ka’idojin Tajwidi da sauti mai dadi.

Kira’ar El Minshawy, Abdul Basit, Mustafa Ismail, da Al-Hussary,  gaba ɗaya ana ɗaukar su a matsayin mafi mahimmanci kuma masu shahararriyar kira’a a wannan zamani da ta yi tasiri sosai a duniyar Musulunci.