Kudin Crypto: Shin An Rufe Binance Ko Dakatar Da Shi A Najeriya?

Wasu yan Najeriya da dama sun yi ta kiraye-kirayen a rufe shafin yanar gizon Binance a Najeriya a yan kwanakin bisa dalilin hauhawar farashin dalar Amurka, inda har dalar ta kusa kaiwa $1/₦2,000.

Mene Ne Binance?

Binance fitaccen dandali ne a duniya na harkar cinikayyar kudaden dijital, (kudin da ba’a gani a zahiri), wato Cryptocurrency. Ayyukan Binance sun hada da sayen kudin na dijital domin ajiyewa har zuwa gaba domin samun riba mai yawa, wato (investment), da kuma siya idan farashin ya tashi wani dan abu ya shigo sai a sayar, wato (trading).

Daya daga cikin mafi darajar kuɗin da ake musaya ko ajiyewa a Binance shine kudin dalar Amurka, da ake kira USDT a dandalin musayar kudi na dijital. Akasarin kamfanoni da daidaikun mutane suna karbar USDT a matsayin hanyar biyan kudi, kuma ita ce hanya mafi girma a fadin duniya.

Batun Rufe Binance A Najeriya

Kawo yanzu Binance yana aiki a Najeriya lafiya lau, kuma ba’a rufe shi ba, amma sai dai ana ta kiraye-kirayen cewa a rufe shi a kasar domin shi ke haddasa hauhawar farashin dalar Amurka wacce ke shafar farashin sauran kayayyaki a fadin Najeriya.

Sannan kuma, idan ta tabbata za’a rufe Binance a Najeriya, babu shakka Binance zasu sassauta hanyoyin da dole ma sai ɗan Crypto daga Najeriya ya samu ‘shiga’ shafin ko manhajar su. Ko Binance ba suyi komai ba, sai an samu mafita, domin fasaha ta ci gaba.

Idan ba’a manta ba, da aka rufe saka kuɗi a Binance ta hanyar amfani da katin ATM a shekarar 2021, sai aka samu samu P2P (tsara da tsara), a yanzu dukkanin mu mun mafi aminta da P2P fiye dukkan wani tsarin mu’amala ta kuɗi a Crypto.

Saboda haka, Binance har yanzu yana aiki a Najeriya, kuma koda rufewa zata faru, dole za’a samu mafita a ciki gaba harkar.