Katse Layukan Glo Zuwa MTN: Ba’a Biyar Mu Bashin Ko Sisi – Globacom

Kamfanin sadarwa na Najeriya, Globacom Ltd, ya musanta zargin da ake yadawa na cewa abokin karawarsa, MTN na bin shi bashin kudin caji a tsakanin su.

Musanta hakan ya biyo bayan sanarwar da hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce za a hana masu amfani da Glo yin kiran waya zuwa ga masu amfani da layin MTN saboda kudaden da ake bin Glo na huldar kira a tsakanin su (interconnect).

Sanarwar wadda Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Reuben Muoka, ya bayar, ta bayyana cewa kamfanin na Glo ya gaza biyan basussukan da ake bin shi duk da yunkurin sasantawa da aka yi ta yi.

Har ila yau, ya bayyana cewa bayan nazarin aikace-aikacen da kuma yanayin da ya shafi bashi, Globacom ba shi da dalilai masu mahimmanci ko dalilai na rashin biyan kuɗin haɗin gwiwar a tsakanin su.

Sanarwar ta kara da cewa, “An bukaci dukkan masu amfani da layin waya da su lura cewa hukumar ta amince da yanke huldar Globacom da MTN.”

“Wannan yayi daidai da sashe na 100 na dokar sadarwa ta Najeriya (2003) da sakin layi na tara na ka’idojin da aka tsara don bada izini don katse haɗin gwiwar ma’aikatan sadarwa (2012).

“A karshen kwanaki 10 daga ranar 8 ga Janairu, 2024, masu amfani da Globacom ba za su iya yin kira zuwa MTN, ba amma za su iya karɓar kira daga MTN.”

Sai dai wani jami’in Globacom da ya so a sakaya sunansa a ranar Talata, ya shaida wa manema labarai a Legas cewa kudin da ya kamata a biya ya kai Naira biliyan N1.6 kuma an biya su ba tare da wata gardama ba.

Jami’in ya ce kamata yayi a yi binciken gaskiya kafin sanar da cewa MTN na bin Globacom bashin.

“MTN bai bin mu kudin wani cajin haɗin gwiwa,” in ji jami’in Glo, ya kara da cewa Glo shi ne kamfanin sadarwa na farko da ya fara fito da biyan kuɗin kiran na kowane sakan a Najeriya, wanda hakan yasa sauran kamfanonin kasashen waje da ke aiki a Najeriya ke bin ka’idar a yanzu.