Kasuwanci

Kashe-Kashen Kasuwancin Crypto 5 Da Yadda Suke Aiki

Zamu iya rarraba kasuwancin Cryptocurrency zuwa gidaje a kalla hudu 4 zuwa 5.

  • Trading
  • Holding
  • Scalping
  • Staking
  • Arbitrage Trading

TRADING

Trading wani kashi ne na Crypto wanda yake bukatar ilmi mai zurfi. Trading na nufin shiga kasuwa a yi sayayya domin a samu riba cikin kwanaki kadan ko kuma awanni kadan.

Trading yana bukatar ilmi ne domin dole sai ka nutsu ka san Token din da zai iya baka riba a kusa. Zaka iya sanin hakan ne ta hanyar bincike ko kuma idan kaji ana maganar wasu sun sayi wani Token na makudan kudade ko kuma an zuba hannun jari a wani Token.

Wadannan duk abubuwa ne da zasu iya sanyawa Token/Coin darajar shi ta daga.

Mai yin trading burin shi a koda yaushe shine ya shiga kasuwa ya fita da wuri. Idan aka sami akasi kasuwa ta bada matsala, to masu Trading zasu iya yin asara wanda zai sa dole su yi zabin dayan-biyu; ko dai su dauki asara ko kuma su jira har lokacin da kasuwar tayi kyau.

Zaka iya yin Trading idan kana bukatar wasu yan kudade da zaka yi yan bukatun ka ko kuma domin kudaden ka su dan karu kayi wani abun da ribar da ka samu.

A wane dandali ya kamata ayi Trading?

Kamar yadda bayanan mu na baya suka nuna, ana yin Trading ne domin a bi wata riba koda babu yawa. To tunda haka ne, kana bukatar Wallet/Exchanger mai saukin caji.

Idan kayi amfani da Exchanger mai yawan caji wasu lokutan sai kaga sun tafi da yar ribar da aka samu.

HOLDING

Holding wani kashi ne shima na kasuwancin Crypto wanda yake bada damar ajiye kudade na tsawon lokaci. Ana yin holding ne da kudaden da ba’a bukatar su a kusa. Mafi yawancin masu holding suna da wani buri ko kuma farashi da suke so a kai wannan gabar kafin su sayar da wannan Token/Coin din.

A lokacin da zaka sayi Coin baka bukatar sai ka banbance holding zaka yi ko trading, amma a zuciyar ka ka san wane irin tsari zaka bi. Holding yana farawa daga wata daya zuwa shekaru. Masu yin holding kusan basa za’a iya cewa basa yin asara domin zasu iya jira na tsawon lokaci har muradin su ya cika.

Scalping

Scalping ma kamar trading ne, yana bukatar ilmi mai zurfi. Scalping wata irin kasuwa ce da ake shiga a fita cikin mintuna ko sakanni ko kuma awanni. Ana yin scalping ne idan aka ga wani Token/Coin yana tashi sosai. Idan ka fuskanci haka sai ka shiga, da zarar ka ci riba ko babu yawa sai ka fita, idan ya kara sauka ka kara shiga.

Wasu lokutan ana yin asara a Scalping idan aka yi rashin sa’a wasu suka sayar da wannan Token din mai yawa wanda hakan zai iya kaiwa ga mummunar asarar da ba’a yi tsammani ba kuma za’a iya daukar lokaci kafin a mayar da wannan asarar ko kuma a hakura a sayar dashi a fadi.

STACKING

Stacking shine kulle sulalla domin a ringa samun wani kasafi. Wannan kasafin ana kiran shi da INTEREST (kudin ruwa). A yaren Crypto ana kiran ribar da ake samu da INTEREST to amma a zahirance ba kudin ruwa bane.

Dalilin da zai sa ba zai zamo kudin ruwa ba shine: ana juya kudin ka ne sai a raba ribar da kai.

Yadda ake Staking

Wasu sun yarda da wannan tsarin ne wajen samun wani kaso na kudi ta hanyar kulle dukiyar su.
Stacking yana da karancin asara.

ARBITRAGE TRADING

Arbitrage Trading kuma ya bambanta da sauran, shi wata hanya ce da ake siyan kudaden ketare a farashin bankuna sannan a sayar a farashin kasuwar bayan fage (P2P).
Hakan yana bada damar samun wasu yan canjika a nan take.

Misalin wannan kasuwar shine; ka sayi USD a N470 ka sayar a N550. Hakan zai baka damar samun riba da zarar ka sayar.

A karkashin Arbitrage Trading akwai TRIANGULAR ARBITRAGE. Triangular Arbitrage shi kuma ana sayen Coin ne a Exchanger daya sannan a juya shi a sayi wani domin a samu riba. Hakan yana faruwa wasu lokutan idan aka sami sa’a sai a sami riba a ciki.

Misali a Binance idan ka sayi BNB da TUSD, sannan ka sayar BNB din ka mayar da shi USDT, za’a iya samun riba idan canjin ya bada dama.

A wasu lokutan kuma ana tura wani Token din zuwa wata Exchanger din idan aka ga sauyin farashi, sai a sayar a waccan Exchanger din. Bugu da kari, ana iya yin irin wannan Triangular Arbitrage din ta hanyar amfani da ORDER BOOK ko kuma STOP-LIMIT.