Kasuwanci

Kamfanoni Sun Shirya Karya Farashin Siminti A Najeriya

A daidai lokacin da farashin siminti ya tashi a Najeriya, masana’antun da ke kera simintin sun bayyana shirin durkusar da farashin tsakanin N7,000 zuwa N8,000 kan ko wane bugu ɗaya.

Kamfanonin kera siminti sun bayyana hakan ne a wani taro da David Umahi, ministan ayyuka na kasa ya kira, wanda ya samu halartar jama’a daga ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, ciki har da ministar, Doris Uzoka-Anite, a Abuja ranar Litinin.

A wajen taron, an yi kokarin gano dalilan da suka haddasa hauhawar farashin kayayyaki ba zato ba tsammani.

Don haka, masana’antun da suka halarci taron suma sun bayyana aniyarsu ta rage farashin nan gaba da zarar gwamnatin tarayya ta cika.

Kamfanonin BUA sun kuma bayyana shirin kawo tan miliyan shida na siminti a kasuwa domin rage tashin farashin kayayyaki.

Gwamnatin tarayya ta kuma bayyana aniyar ta na karfafa gwiwar kafa sabbin masana’antun guda shida.

Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da farashin siminti ya yi tashin gwauron zabo zuwa sama da N10,000 kan ko wane kilogiram 50 a babban birnin tarayya.

Tun da farko, shugaban kungiyar masu sana’ar siminti ta Najeriya, CEPAN, Prince David Iweta, ya bayyana cewa bukatar siminti ya fi karfin samar da shi a dalilin tashin farashin.

Advertisement