Addini

Idan Likita Yayi Sanadiyar Mutuwar Mara Lafiya, Shin Zai Yi Kaffara?

Tambaya?

Assalamu alaikum, Malam don Allah ina da tambaya ni Nurse ce to ina aiki aka kawo min mara lafiya (Patient) mai matsalar ‘Respiratory Distress’ na daura shi saman ‘Oxygen Therapy’ kuma yake min cewa yana jin ciwo, ya rasa inda zai sa kan shi ya ji dadi, sai na kira Doctor don ya zo yaji korafin, na jira bai zo ba, sai na ruba ta mashi Paracetamol Injection da Diazapem don ya samu yayi bacci, ina ba shi Injection din sai Condition din ya chanza sai ya fara sheɗa ɗaya-ɗaya ‘Gasping’ bai dade ba ya ya rasu, na san lokacin shi ne yayi, amma sai ni ke tunanin ko Injection din da na ba shi ita tasa ciwon ya kara rikecewa, sai na yi Browsing a Internat sai na ga ashe ba’a yi ma mai ‘Respiratory Distress’ allurar Diazapem.

Tambaya ta shine zan yi azumin kaffara ne koko tun da ni nayi ne don in taimake shi ban san tana da illa ba? Nagode.

Amsa;

Wa’alaikumus-ssalam,
Za ki yi kaffarar kisan kuskure saboda a Ka’idar likitanci Nurse ba sa bada magani ko Allura sai da iznin likita ko shiryarwarsa, ke kuma kin kuskure kin ba shi maganin da bai kamata ya sha ba kafin likitan ya zo, kamar yadda kika yi bayani, don haka ke ce kika zama sababin mutuwar shi.

Rayukan mutane amana ne, ya wajaba Likitoci su yi taka-tsantsan wajan zama sababin salwantar su, gushewar dakin Ka’aba ya fi sauki a wajan Allah fiye da kashe Musulmi.

Haka zalika, Idan likita ya yi sakaci wajan TIYATA, ko kuma hada magani ko ya kuskure wajan abin da ya kamata, har Mara lafiya ya mutu, zai yi kaffara, saboda kisa ne na kuskure, kisan kuskure kuma ana yi masa kaffara kamar yadda Allah ya yi bayani a aya ta (92) a Suratun Nisa’i.

Za ki yi kaffara ta hanyar biyan diyyar rai da kuma Azumin watanni biyu à Jere.
Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

23/01/2020