Hirar Wani Babban Manomi Mai Hikima Da Jan Jarida

Akwai wani manomi da ya shuka masara mai kyau. Duk shekara yakan lashe kyautar masara mafi girma. 

Shekara ɗaya wani ɗan jarida  ya yi hira da shi kuma ya koyi wani abu mai ban sha’awa game da yadda ya ke noma masarar shi.

Dan jaridar ya gano cewa manomi yana bai wa makwabtan shi irin masarar shi.

“Ta yaya za ka bai wa makwabtan ka wannan irin masarar mafi kyawu, bayan duk kuna shiga gasar noma  masarar a tare kowace shekara?”  dan jaridar ya tambayi manomin.

”In ji manomi, “Ba ka sani ba?  Iska takan dauko lalattaccen irin masara daga cikin masarar da ta nuna tana jujjuya shi daga gona zuwa gona. 

Idan maƙwabta na sun noma masara kadan za ta lalata ingancin masara ta a hankali. Idan zan yi noman masara mai kyau, dole ne in taimaki makwabta su noma masara mai kyau kada iska ya dauko lalattaccen iri ya lalata masara ta.”

Haka rayuwar mu take… Masu son yin rayuwa mai ma’ana da kyau dole ne su taimaka wajen wadatar da rayuwar wasu, domin ana auna darajar rayuwa ta hanyar rayuwar da ta taimaka. Kuma waɗanda suka zaɓi yin farin ciki dole ne su taimaki wasu su sami farin ciki, domin jin daɗin kowannen su yana tattare da jin daɗin kowa.