Hanya Ɗaya Tilo Mafi Sauri Da Sauƙi Don Tantance Jabun Kuɗi Da Na Kwarai
Yan kwanaki kadan bayan fara amfani da sabbin takardun kudi da suka haɗa da Naira ₦200, ₦500 da ₦1000, mutane da dama na cikin fargabar fada wa hannun yan damfara masu yawo cikin al’umma domin cuta ta hanyar sayen kaya da kuma bayar da kudin jabu (Fake) ga masu sana’o’i, musamman a kauyuka.
Saboda haka wannan shafin yanar gizo na Arewa Times ya dauki aniyar fadakarwa da ilmantar da jama’a ta yadda zasu gane jabun kuɗi cikin sauri da sauki.
Idan kuka yi dubi da hoton da de cikin wannan labarin, za ku ga cewa in fitar wasu wurare a kan sabbin kudin, to wadannan wuraren sune hanya mafi sauri da sauki domin h’gane kuɗi na bogi.
Idan ka karbi kuɗin, kuma kana shakku akan kudin, kawai kayi amfani da babbar yatsar ka ta hannu sai karkari wadannan wuraren da muka fitar sosai. Idan ka fara ganin fentin da ke a wuraren ya fara gogewa, to hakan na nufin kuɗin ba kwarai ne ba, jabu ne.
Bayan wannan, zaka kuma iya saka yawu wuraren sai ka goga a hankali, shima haka zai sa idan ba kudin kwarai ne ba, to fentin zai goge.