Kasuwanci

Farashin Bindiga, AK-47 Ya Faɗi A Kasuwar Bayan Fage A Sudan

Farashin bindiga kurar AK-47, wacce tana daga cikin makaman yaƙin da aka fi amfani da su a faɗin duniya ya faɗi warwas da kashi 50% cikin 100% a watannin da suka gabata a kasuwar bayan fage dake Khartoum babban birnin kasar Sudan wacce tashe-tashen hankula ya ɗaiɗaita, domin a yanzu ana AK-47 akan kuɗin Amurka dala $830.

Wani dillalin makamai ya ɗora alhakin faɗuwar farashin bindigar kan yadda bindigar mai laƙanin Kalashnikov ta ƙasar Rasha ta cika kasuwannin bayan fage bayan ɓallewar rikici a Sudan a watan Afrilu.

Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojoji da dakarun RSF a kan titunan biranen Khartoum da Bahri da kuma Omdurman waɗanda sune manyan biranen ƙasar.

Wani mai saye da sayar da bindigogi ya bayyana cewar ya na sayen bindiga daga tsoffin sojoji waɗanda da dama daga cikinsu dakarun RSF ne a yanzu.