Kasuwanci

Kurakuran Da Yan Najeriya Suka Gani Ga Sabbin Kudin Suka Cira A Banki

‘Yan Najeriya sun mayar da martani ta hanyar amfani da shafin su na sada zumunta na zamani suna raba sabbin takardun Naira da aka ba su a bankunan su daban-daban.

Ku tuna cewa babban bankin Najeriya a hukumance ya gabatar da sabbin takardun kudi na Naira a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022 a fadin kasar nan. An ce sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1000 da aka bullo da su zai yi wuya a yi jabu.

Yayin da tsofaffin da sabbin takardun naira suna nan a yanzu. A ranar 31 ga watan Junairu, 2023 ne dai wa’adin tabbatar da tsohuwar takardar Naira ta kasance, an kuma umarci ‘yan Najeriya da su je su yi musaya da dukkan tsoffin takardun nasu zuwa sabbin takardun naira da ke banki kafin cikar wa’adin.

A yayin da ‘yan Najeriya ke yin haka, wasu ‘yan Najeriya sun yi ta yada wasu sabbin takardun kudi na Naira da suka nuna ba su da kyau a cikin sabbin takardun Naira da aka ba su a banki.

Kamar yadda aka gani a Hotunan da suke zagayawa a shafukan sada zumunta, ba a yanke wadannan sabbin takardun Naira yadda ya kamata ba. Ɗaya daga cikin sababbin sababbin takardun naira shine takardar N500 wanda ba a yanke daidai ba da ma’aunin da ya dace ba. Haka kuma akwai takardar N1000 wadda ta wuce kima a cikin yankan.

Wannan ya haifar da martani daga masu amfani da yanar gizo yayin da suke bayyana ra’ayoyin su daban-daban a kai.