Dangote Ya Samu Ribar Sama Da Miliyan $100 A Kwanaki 7 Na Farkon 2024

Attajirin dan kasuwan nan na Najeriya, Aliko Dangote ya samu wani gagarumin sauyi na harkokin kudi, inda ya samu ribar sama da dala miliyan $100 a makon farko na shekarar 2024, ya kuma kara habaka darajar dukiyar shi da fiye da dala biliyan $15, biyo bayan faduwar dala biliyan $3.6 a shekarar 2023 da ya samu.

An yi la’akari da haɓakar dukiyar shi na saka hannun jari daban-daban a kan kasuwar musayar kudi ta Najeriya (NGX), wanda ke haifar da canjin kasuwa mai ban sha’awa wanda ya haifar da ginshiƙi na babban rabo na kasuwanci kusa da matakin maki 80,000.

Arzikin Dangote, wanda cibiyar Bloomberg Billionaires Index ta binciko, ya karu daga dala biliyan $15.1 a farkon shekarar 2024 zuwa dala biliyan $15.2 a lokacin rubuta wannan rahoto – karuwar dala miliyan $106 da dukiyarsa ta samu a bana na da nasaba da yadda jarin shi ke haɓaka a kasuwar NGX.