Kasuwanci

Dan Kabilar Igbo Ya Kaddamar Da Kamfanin Sufurin Jiragen Sama, United Nigeria

Wani hamshakin dan kasuwa wanda ya rikide ya koma dan siyasa a yankin kudu-maso-gabas (South-East) a Jahar Anambra dan kabilar Igbo mai suna Dr. Obiorah Okonkwo ya kaddamar da kamfanin sufurin jiragen sama a Najeriya mai (United Nigeria) a turance, wanda ke nufin (A hada kai Najeriya).

Idan zamu iya iya tunawa hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa a yan watannin baya ta baiwa Dr. Okwonko takardun damar kafa kamfanin harkokin kasuwanci na sufuri, yayin da kamfanin ta soma aikin jir-jirgar fasinjoiji a jiye Juma’a.

Haka zalika wasu yan kabilar ta Igbo sun sha alwashin ba zasu yi amfani da jiragen Dr. Okwonko ba domin tafiye-tafiyen su ba saboda sunan (A hada kai Najeriya) da ya sanyawa kamfanin na sa, inda suka bayyana cewa kan Najeriya ba a hade yake ba.

Advertisement