Kasuwanci

Bankin Kayi: Hanyar Turawa Da Karbar Kuɗi Mai Inganci

Bankin Kayi wani sabon bankin intanet ne domin turawa da karbar ba tare da wani shamaki ba. Manhajar Kayi, aikace-aikacen banki na dijital ne, wato yanar gizo, kamar Opay ko PalmPay.

Yin amfani da ƙarfin fasahar Gidan Yanar Gizo web3, Kayi yana ƙirƙira tsarin yanayin harkokin kuɗi tare da manyan hanyoyin tsaro ta yanar gizo.

Babban burin manhajar Kayi shine canza tsarin banki na zamani.
Dandalin yana ba da cikakkun ayyuka na harkokin kuɗi waɗanda suka dace da bukatun kuɗi na masu amfani da shi.

Daga cikin su akwai zuba hannun jari, kariyar inshora, zaɓuɓɓukan lamuni masu amfani, amintaccen musayar cryptocurrency, da shirin tanadi na musamman wanda ke ba da tabbacin samun riba mai yawa.

A Kayi, jin daɗin ku yafi mahimmanci. Shi yasa suka yi farin cikin sanar da kaddamar da Hedkwatar su a Kano, wannan alama ce ta sadaukar da kai ga abokan ciniki.