Kasuwanci

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Bankunan Yanar Gizo, OPay, PalmPay

Bankunan yanar gizo, ko kuma Mobile banking a turance, bankuna ne zamani waɗanda Babban Bankin Najeriya CBN ya yiwa ragista kuma suna lasisin insura daga NCDI. Hakan na nuna cewa bankunan ba guduwa zasu yi ba, kuma CBN ba zai rufe su ba, saɓanin yadda wasu mutane ke yaɗa jita-jita maras tushe akai.

Sannan kuma, koda kuwa an rufe maka OPay, ko PalmPay account saboda baka saka BVN ko NIN naka ba, hakan ba bawai yana nufin ka rasa account din da kuɗin ha abada ba ne. Sannan OPay, PalmPay ko Kuda bank ba zasu gudu ba, hasalima sune mafi sauki a gare ka.

Koda an rufe maka account dinka saboda rashin saka BVN zasu baka damar kayi providing BVN ɗin ka, ko NIN ɗin ka domin cigaba da amfani dashi, kana saka masu BVN dinka shikenan zai bude. Shi yasa saka masu BVN din tun kafin su rufe yake da muhimmanci, saboda tun farko kai kasan bude account ba tare da ka saka wani Identification ɗin ka ba, is Illegal.

Dalilin haka, dole sai wata rana an bukaci identity na ka, kuma ko a wurin bude accounts din suma suna sanar da kai ka saka BVN ɗin ka, sai dai suna bada damar hakan ne a matsayin Optional domin matakai na kasuwanci irin na su, amma duk da ran dadewa dole sai ka saka Identity ɗin ka.