Al'umma

Zina: Abubuwa 9 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ita

Zina iri-iri ce, kashi-kashi kuma – Wata tafi wata muni.

1. Yin zina da uwa ko ƴar’uwa ko ƴa, da dukkan maharramai, wannan ita ce mafi muni a cikin alfashar zina, wanda ake hukuncin kisa ga wanda ya aikata haka.

2. Yin zina da matar aure matar maƙwabci, wannan zina ce tare da cin amana, akwai haƙƙin Allah da haƙƙin maƙwabci da haƙƙin aure. Kuma alhakkin shi kamar ya yi zina sau goma za a rubuta masa, idan haka ya tabbata.

3. Yin zina da matar aure da miji mai aure, wannan akwai alhakki da yawa akan su sosai, na cin amanar aure da keta alfarma shi kuma ga hukuncin kisa ta hanyar jefawa a kansu. Idan an kama su, in hakan ya tabbata.

4. Yin zina tsakanin mai aure da mara aure, ɗaya yana da hukuncin kisa ɗaya yana da hukuncin bulala ɗari da ɗaurin shekara a gidan yari, in hakan ya tabbata.

5. Yin zina tsakanin bazawari da bazawara, duk sun aikata babban laifi kuma idan shedu suka tabbata a kan su, su lna da hukuncin kisa ta hanyar jefewa a addinin musulunci.

6. Yin zina tsakanin saurayi da budurwa, waɗanda ba su taɓa yin aure ba, hukuncin su, bulala da kuma ɗaurin shekara a wani gari ga namijin kawai, in hakan ya tabbata.

7. Yin zina ko fyaɗe ga ƙaramar yarinya, wannan yana da muni sosai da gaske, kuma wasu daga cikin malamai suna ganin hukuncin kisa ga wanda ya aikata haka, in an tabbatar.

8. Zina wata babbar musiface da bala’i da dukkan sharri, da take ruguza al’umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da annoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.

9. Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka:

  • Raunin Addini
  • Raunin Akida
  • Karancin Imani
  • Rashin kunya
  • Rashin kishi

    Advertisement