Illolin Mining Na Crypto Coins A Cikin Al’ummar Musulmai
KADAN DAGA CIKIN ILLAR MINING NA CRYPTO COINS A CIKIN AL’UMMAR MUSULMAI
Na san dole wasu zasu zage ni akan wannan zancen, amma hakan bazai hana ni na fada musu gaskiya ba game abinda na hango ba a cikin dan karamin sani na ba.
Ku tsaya sosai kuyi nazari, mining kirifto yana da manufofi kamar haka.
- Dauke hankalin musulmai game da kisan mu da ake wadda Kuma kowa ya sani kashe-kashe da ake a Nigeria akwai shiri a ciki daga ciki da waje. Wadda Kuma kullum abubuwa kara tabarbarewa suke.
- Dauke hankalin mu wajen kulawa da addini.( Karatun Kur’ani, Azkar, Nafila, sauraron wa’azi).
- Koyawa mana lalaci da nufin samun kudi ba tare da shan soaai wahala ba.
- Halasta mana kudi kowane iri ba tare da tantance halak da haram ba.
- Daukaka darajar manufofin Yahudawa a dalilin sun ba ka hanyar samun kudi cikin sauki.
- Cusawa yara akidar amfani da waya wadda hakan kan hana yara yin karatu.
- Koya mana raina sana’o’i, musamman kananan sana’o’i, kamar kafinta, makanike, tela, yankan farce da sauransu.
- Rashin kulawa da Mazaje daga matar aure .
- Rashin bai wa mata lokaci daga mazajen su da kuma raini a gidajen aure.
- Rashin kulawa da kuma bada muhimmanci ga mai sana’a (a kasuwa ko shagon shi).
- Samun gazawa daga ma’aikatan gwamnati, sakamakon mining domin neman kuɗi a saukake.
- Saka buri a zuciya a kan abin da ba shi da tabbas kuma ba mallakin ka ba.
Wadannan kadan kenan daga ciki, na sani wani zai ce min dan kauye, ko kuma ban waye ba, to sai dai a fada domin har a raina ban yarda da wannan tsarin ba gaba dayan shi ba.
Ina kawo abubuwan samun kudi sosai zuwa ga al’umar mu ta hausa, Amma nafi gamsuwa da kayi kasuwanci kasa mi kudi.
Dalili na anan shi ne, ta yaya wani zai ba ka kudi ba tare da wata manufa da yake son cimma Kansa a kanka ba?
Yahudawa a duk duniya ba su da abin gaba kamar musulmai, da kuma bakar fata, to ta yaya zasu so ku amfana da arzikin su haka kawai?