Al'umma

Zan Sake Ki Idan Ke Ba Ni N320,000 – Miji Ya Fada Wa Matar Shi Da Kotu

Wani dan kasuwa, Musa Usman, a ranar Larabar da ta gabata ya roki wata kotun shari’a da ke Kaduna da ta umurci matar shi mai neman saki, Aisha Umar ta biya shi Naira 320,000 domin samun ‘yancin ta.

Usman, ta bakin lauyan shi, Safiyanu Saleh ya ce duk da cewa yana son matar shi, amma ba zai hana ta aiwatar da hakkin ta na saki ta hanyar Khul’u.

“Na biya sadaki N70,000 amma ina so ta kara N250,000 domin in auri wata mata” inji shi.

Tun da farko, mai shigar da kara ta bakin lauyan ta, Abubakar Sulaiman ta roki kotun da ta raba auren ta da Usman ta hannun Khul’u.

Sulaiman ya ce yanzu matar ba ta da sha’awar auren, kuma a shirye take ta maido mata sadakin Naira N70,000 da ta karba a wurin shi ko kuma kasa da haka.

“Kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, mace za ta iya fanshi kan ta daga aure ta hanyar biyan sadakin da ta samu, ko sama da haka; don haka muna rokon ta karawa kudi saboda tabarbarewar tattalin arziki.

“A madadin haka, muna rokon ta ciyar da lokacin jiririn ta wanda shine sau uku a kowane wata a maimakon N70,000”, in ji shi.

Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai ya dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Janairu domin yin jawabi na karshe na bangarorin biyu tare da yanke hukunci.

Lokacin jira da aka fi sani da iddah wata al’ada ce da mace za ta kiyaye bayan mutuwar mijin ta ko bayan rabuwar aure, wanda ba za ta auri wani namiji ba.

(NAN)