Yadda Za’a Sayi Data Akan MTN, AIRTEL, GLO Da 9MOBILE
Na san cewa wannan maganar ta yadda za’a sayi Data domin Browsing zai zama abin dariya ga wasu, haka zalika a wajen wasu abu ne wanda ya daɗe yana ci musu tuwao kwarya.
Data a yanzu ta kasance rayuwa ce ga masu amfani da wayoyin zamani na Android, da sauran su.
Mutanen da suka saba amfani da Data wajen shiga shafukan sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp da sauran su, abu mai wuya ne gare su ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da sun shiga yanar gizo ba, wato Internet.
Kasancewar ba kowa ba ne ya san dukkan komai, abin da yake da sauki a wajen wani, haka wannan abin yake da wahala ga wani, saboda haka zamu bayyana wa masu karatu yadda zasu sayi Data akan layin MTN, AIRTEL, GLO da 9MOBILE da sauransu.
Akan layin ka na MTN, Airtel, Glo, 9Mobile, Visafone da sauransu, sai ka danna *312#. Wannan code yana akan dukkan layukan waya a Najeriya kamar yanda hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa.