Al'umma

Yadda Wani Malami Ya Sace Ɗalibar Shi Yayi Mata Gunduwa-Gunduwa

Datti Assalafiy:

Hakika zuciyata ta kadu matuka da jin labarin garkuwa da wannan yarinya Hanifa a jihar Kano da kuma kashe ta da akayi kisan wulakanci.

Wanda ake zargin yayi garkuwa da yarinyar Shugaban Makarantarsu ne, Malamin da ake zargi ya mata kisan wulakanci ya bunne gawarta a gurin karban kudin fansa aka kamashi yaje ya nuna inda ya bunneta aka tono gawarta aka mata jana’iza.

Malamin da wadanda suka taimaka masa, sun mata kisan wulakanci, sun sanya mata guba a cikin shayi suka bata ta sha, bayan ta mutu sai suka daddatsa gawarta suka je suka bunne.

Matsalolin garkuwa da mutane yana cigaba da canza salo, indai har Malami zai iya yin garkuwa da Dalibarsa kamar wannan to hakika masifar ta kai masifa, kuma wannan darasi ne garemu iyaye da muke tura yaran mu makaranta.

Ya kamata a zartarwa wannan Malami da wadanda suka tayashi mummunan hukuncin kisa a bainar jama’a domin ya zama babban darasi ga masu tunanin aikata mugun laifi irin nasa.

Allah Ka jikan Hanifa