Al'umma

Mafarauci Ya Harbe Wani Mutum Har Lahira Bisa Tunanin Cewa Tsuntsu Ne A Kano

Da sanyin safiyar yau ne, kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta rawaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani mafarauci mai suna Muhammadu Basiru dan shekara talatin da biyu (32) bisa zargin kashe wani a lokacin da yake kokarin harbin wani tsuntsu a daji.

Da yake bayyana mummunan lamarin, maharbin yace, “Ban gudu ba bayan harbe shi ba. Na dauka tsuntsu ne a cikin daji.” Mafarauci ya ba da labarin yadda ya kwashe sama da shekaru shida yana farauta da bindigar ahi. Ya kara da cewa, “A ranar da na mayar da hankali na shi ne in harbe tsuntsun saboda ban lura cewa wani yana kusa da tsuntsun ba.”

A karshe Muhammad Basiru yace, “Nan da na harba harbi ne na ji wata babbar kukan daji, da na isa wurin, nan take na nemi a taimaka min.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin domin sanin matakin da za a dauka na gaba.

Mene ne ra’ayinku game da kisan da ake zargin wannan mafarauci ya aikata?