Yadda Hafsat Ta Kashe Nafi’u Da Wuka

A kwanakin nan wani abin baƙin ciki ya farua jihar Kano, inda wata matar aure mai suna Hafsat ta hallaka wani saurayi da aka yaron mijinta ne Dayyabu, mai suna Nafi’u wanda kuma gefe ɗaya ake zargin cewa tsohon saurayinta ne ta hanyar caka masa a kirji da sauran sassan jikin shi sau da dama.

Kamar yadda aka yi zargi, bayan Hafsat ta yi aure sai suka haɗa hulɗar kasuwanci tare da Nafi’u, har ita Hafsa ta buɗe shago a Zoo Road, yayin da Hafsat da mijinta Dayyabu suke zaune a wani karamin gida lokacin da suke kasuwancin da Nafi’u.

Bayan wani lokaci sai mijinta ya gina babban gida kafin domin su koma can tare da matar shi, kafin wannan lokacin komawar, an bayyana cewa Hafsat ta haɗa mijin nata da Nafi’u har suna harkoki a tare.

A lokacin da su Hafsat zasu tare a sabon gidan su an yi zargin cewa ta ce mijinta dole sai dai a koma sabon gidan tare da Nafi’u, haka mijin ya amince ance da shawarar ta.

Bayan komawa a sabon gida da wani lokaci, sai Nafi’u ya kamu da rashin lafiya har iyayensa suka zo a Kano daga Jihar Bauchi har ya ga Dayyabu mijin Hafsat a matsayin maigidan shi ga kasuwanci ga iyayen shi. Haka zalika an yi zargin cewa ba kowa yasan cewa Nafi’u tsohon saurayin Hafsat ba ne, sai abokan Nafi’un da kawayen ita Hafsat.

Bugu da kari, an yi zargin cewa, ko ina Hafsat zata tafi tare suke tafiya da Nafi’u har aikin Umrah, kuma ba tare da ya ce komai ba.

An yi zargin cewa kuma, Hafsat ta kashe Nafi’u ne dalilin ya faɗa cewa ya samu matar da zai aura, amma Arewa Times Hausa bata samu ingancin wannan zargin ba.

Amma kuma, a jawabin da ta yiwa hukumar yan sanda ta jihar Kano, Hafsat ta bayyana a lokuta da dama ta yi yunkurin kashe kanta, amma shi Nafi’u ne hana ta hallaka kanta. Sai a wannan karon lokacin da ta dauko wuka zata hallaka kanta, a yunkurin Nafi’u na kwace wukar da ke hannunta sai yanke hannunta, sai Nafi’u ya ce mata ta je canja tufafi ta wanke hannun.

Ta kara da cewa: Bayani na fito daga bayi, Nafi’u yana a kwance kan kujera, sai na lallabo na ɗauki wukar na caccaka masa cikin wani yanayi ban saba jin kaina a ciki ba.

Har yanzu rundunar yan sanda na ci gaba da bincike domin bankado masu laifi a lamarin domin gurfanar da su a gaba kotu.