Yadda Ake Haɗa Maganin Farin Jini

Jama’a barka da wannan lokaci, da fatan kuna lafiya. A yau zamu yi dan bayani game da farin jini da kum yadda ake haɗa maganin farin jini.

Mene ne farin jini? Farin jini shi ne al’umma ko mutane su riƙa samun farin ciki ko son ganin wani mutum a cikin lamuran su, idan mutum yana da farin jini kowa zai so haɗa lamuran shi na arziki da shi.

Bayan haka, a kasa zamu yi bayanin yadda ake haɗa maganin farin jini.

Da farko, za’a samu gemun masara, sannan a shanya shi ya bushe. Bayan nan za’a daka wannan gemun masarar ya zama gari.

Na biyu, zamu samu turare mai ƙamshi kowane iri ne, sai a haɗa shi wannan garin gemun masarar a garwaya, sai a rika shafawa idan an yi wanka.

Insha Allah, da yardar Ubangiji wannan zai yi aiki sosai.