Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Mahaifin Wata Budurwa Kan Hana Su Auren Ta

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum a kauyen Kwalfada da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara saboda ya ki aurar da ‘yarsa ga abokin aikin ta’addancin su.

A cewar wani mazaunin unguwar, Usman Magaji, daya daga cikin ‘yan fashin ya nemi auren daya daga cikin ‘yan matan kauyen amma mahaifin yarinyar ya ki amincewa da hakan.

Magaji ya bayyana cewa mahaifin yarinyar ya yanke shawarar aurar da ita ga wani dan kauyen, inda yayi watsi da shawarar barayin.

“Bayan an daura auren, sai ‘yan fashin suka far wa kauyen inda suka kashe mahaifin yarinyar.

“’Yan ta’addan sun kuma bukaci sabon mijin da ya aure ta, da ya gaggauta sakin matarsa ​​domin abokin su ya aure ta.

“Sun yi barazanar kashe mijin idan bai bi umarnin ba.

“Nan da nan sai mijin ya saki matar kuma ta sake auren dan fashin kuma ya kai ta daji,” inji shi.

Magaji ya kara da cewa ‘yan fashin sun dade suna ta’azzara wa al’umma saboda rashin samar da tsaro ga al’umma.

A cewar sa, ‘yan fashin sun rika dora wa al’umma haraji, yana mai nuni da cewa, ‘yan makonnin da suka gabata mutanen kauyen sun biya Naira miliyan hudu.

“Dole ne mu sayar da kayan abincin mu da sauran kayayyaki masu daraja kafin mu tara adadin,” in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abdulahi, bai ce uffan ba game da batun har zuwa lokacin da ake gabatar da rahoton.