Al'umma

Ya Abin Ya Faru? Labarin Matar Da Ta Auri Maza Biyu

Wata mata ‘yar kasar Congo ta baiwa masu amfani da shafukan sada zumunta mamaki inda ta bayyana cewa tana auren maza biyu kuma dukkan su suna zaune tare da ‘ya’yan su.

Francine Jisele tana zaune a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tare da mijinta na farko, Remi Murula, da mijinta na biyu, Albert Jarlace.

Lamarin ya taso ne lokacin da mijinta Jisele na farko ya bace tsawon shekara uku.

A lokacin, ta ƙaunaci Jarlace. Sai dai da Murula ya dawo, Jisele ya ce kada ya tafi, Jarlace, babu inda za ka.

Yanzu, dukan su suna zaune tare cikin jituwa, suna raba nauyi da kuma girmama juna.

Kalubalen da suke fuskanta shine banbance uban yaran.

Jisele ta yarda cewa yana da wuya a gare ta kuma tana fatan kowane daga cikin su ya sami gidan kansa. Ba ta son su kasance tare a ɗakin kwana ɗaya lokaci guda.