Wata Mata Ta Bukaci Kotu Ta Raba Auren Su Bisa Rashin Gamsar Da Ita Akan Gado

Wani Imma Wole ya maka matar shi, Olu, kotu bisa abin da ya yi ikirarin cewa yana damun shi da kin bin umarnin ahi.

Imma ya shaida wa Kotun Al’adu ta Grade A, Mapo, Ibadan, Jihar Oyo, cewa Olu mace ce mai girman kai da damuwa wanda ke jin farin cikin yi masa wulakanci a bainar jama’a sannan kuma tana fada da makwabta.

Tuni dai kotun ta dage sauraren karar saki da Imma ta gabatar.

Imma wanda ya shaida wa kotun cewa ya gaji da zama da Olu saboda babu sauran soyayya a tsakanin su, ya roki kotun da ta hana matar shi daga tursasa shi da yi masa barazana.

Matar, Olu ta amince a raba auren, inda ta bayyana cewa Imma da dangin shi ba su yarda ta sami kwanciyar hankali ba tun da suka yi aure ba.

Wadda ake karar ta bayyana cewa ta dade tana jure auren su ne saboda mijin nata ba shi da karfin jima’i kuma ya kasa gamsar da ita a dakin kwanan ta.

Shaidar Imma ta tafi haka: “Ya shugabana (Alkali), ba na son mata ta kuma. Ina rokon wannan kotu mai daraja ta ruguza auren mu.

“Olu ba ta daraja ni. Ta dafa kafada da ni a cikin gida kuma ba ta bin umarni na yadda aka so.

“Mata ta ta kasance mai al’adar barin gida ba tare da yarda ta ba kuma ba za ta bar wata masaniya game da inda take ba.

“Olu wani lokaci takan kasance ba ta gida na mako guda ko fiye kuma ta kasa bayar da wani gamsasshen bayani idan ta dawo.

“Tana ɗaga muryar ta a kaina a duk lokacin da na nuna rashin jin daɗin na game da rashin ɗabi’ar ta kuma wani lokacin takan yi mini fada.

“Alkalina, mata ta ta taba mari na a cikin rigima, ba ta nuna wata damuwa ba ko da ‘yan uwan mu ne suka shiga tsakani a tsakanin mu.

“Olu ba ta iyakance halin ta na rashin mutunci a gida ba. Ita ma tana zagi da wulakanta ni a cikin jama’a.

“Makwabtan mu ma ba su tsira ba. Ta kara musu halin kiyayya kuma tana yakar su a kowane zarafi, ta haka ta sa rukunin gidan ya zama yamutsi a kowane lokaci.

“Matata ta mayar da ni abin ba’a a harabar mu da unguwarmu. Jama’a yanzu suna min ba’a duk lokacin da na wuce.

“Ya shugabana, ba na son Olu a ƙarƙashin rufi na.

“Ina rokon kotu da ta hana ta tsangwama ko yi min barazana a gida ko ofis.”

Olu ta amsa shaidar Imma ta ce, “Ya shugabana, na haƙura da auren mu sosai. Na yarda ni da Imma mu rabu.

“Mijina da dangin shi sun ƙi su bar ni na huta. Iyalin shi ba su daina tsoma baki a harkokin mu ba.

“Ni da Imma kullum muna cikin rikici ne saboda ya kasa sauke nauyin da ke kan shi na aure a kai na.

“Ban ji dadin auren mu ba saboda karfin jima’i na mijina ba komai bane. Ya kasa gamsar da ni a gadon.”

Shugabar kotun, Mrs S.M Akintayo, ta dage sauraron karar bayan ta saurari bangarorin biyu.